Azkar da addu’o’i iri-iri

Saitunan karatu
دُعَاءُ لُبْسِ الثَّوْبِ
الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي كَسَانِي هَذَا (الثَّوْبَ) وَرَزَقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلَا قُوَّةٍ.
Addu’ar saka tufafi
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya tufatar da ni wannan tufafi kuma ya azurta ni da shi ba tare da dabara ko ƙarfi daga gare ni ba.
دُعَاءُ لُبْسِ الثَّوْبِ الْجَدِيدِ
اللَّهُمَّ لَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ كَسَوْتَنِيهِ، أَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِهِ
Addu’ar saka sabon tufafi
Ya Allah, godiya ta tabbata gare Ka; Kai ne ka tufatar da ni shi. Ina roƙonka alherinsa.
دُعَاءُ الْكَرْبِ
لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ الْعَظِيمُ الْحَلِيمُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ رَبُّ السَّمَاوَاتِ، وَرَبُّ الْأَرْضِ وَرَبُّ الْعَرْشِ الْكَرِيمِ
اللَّهُمَّ رَحْمَتَكَ أَرْجُو فَلَا تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْنٍ وَأَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ
لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ
اللَّهُ اللَّهُ رَبِّي لَا أُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا
Adduar damuwa
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai girma, Mai haƙuri. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin Al’arshi mai girma. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai, Ubangijin ƙasa kuma Ubangijin Al’arshi mai daraja.
Ya Allah, ina fatan rahamarka; kada Ka bar ni ga kaina ko da ƙiftawar ido ne, kuma Ka gyara mini dukkan al’amurana. Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ni na kasance daga azzalumai.
Allah, Allah ne Ubangijina; ba na haɗa Shi da komai.
دُعَاءُ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ
اللَّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ ابْنُ عَبْدِكَ ابْنُ أَمَتِكَ نَاصِيَتِي بِيَدِكَ مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ ، عَدْلٌ فِيَّ قَضَاؤُكَ أَسْأَلُكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ سَمَّيْتَ بِهِ نَفْسَكَ أَوْ أَنْزَلْتَهُ فِي كِتَابِكَ ، أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَدًا مِنْ خَلْقِكَ أَوِ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الْغَيْبِ عِنْدَكَ أَنْ تَجْعَلَ الْقُرْآنَ رَبِيعَ قَلْبِي ، وَنُورَ صَدْرِي وَجَلَاءَ حُزْنِي وَذَهَابَ هَمِّي.
اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ وَالْعَجْزِ وَالْكَسَلِ وَالْبُخْلِ وَالْجُبْنِ ، وَضَلَعِ الدَّيْنِ وَغَلَبَةِ الرِّجَالِ.
Adduar baƙin ciki da damuwa
Ya Allah, ni bawanka ne, ɗan bawanka kuma ɗan baiwarka. Goshina yana hannunka, hukuncinka yana gudana a kaina, kuma ƙaddararka gare ni adalci ce. Ina roƙonka da duk wani suna naka da Ka sa wa kanka, ko Ka saukar a cikin Littafinka, ko Ka sanar da wani daga halittunka, ko Ka keɓance shi a ilimin gaibu da ke wurinka, Ka sanya Alƙur’ani ya zama ruwan bazarar zuciyata, hasken ƙirjina, mai kawar da baƙin cikina da gusar da damuwata.
Ya Allah, ina neman tsarinka daga damuwa da baƙin ciki, gazawa da kasala, rowa da tsoro, nauyin bashi da rinjayar mutane.
دُعَاءُ قَضَاءِ الدَّيْنِ
اللَّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلَالِكَ عَنْ حَرَامِكَ وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكَ عَمَّنْ سِوَاكَ
Addu’ar biyan bashi
Ya Allah, ka wadatar da ni da halal ɗinka daga haram ɗinka, kuma ka wadatar da ni da falalarka daga buƙatar waninka.
دُعَاءُ الرِّيحِ
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا فِيهَا، وَخَيْرَ مَا أُرْسِلَتْ بِهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا فِيهَا وَشَرِّ مَا أُرْسِلَتْ بِهِ.
Addu’ar iska
Ya Allah, ina roƙonka alherinta, alherin abin da ke cikinta da alherin abin da aka aiko ta da shi. Ina neman tsarinka daga sharrinta, sharrin abin da ke cikinta da sharrin abin da aka aiko ta da shi.
دُعَاءُ الرَّعْدِ
سُبْحَانَ اللَّهِ الَّذِي يُسَبِّحُ الرَّعْدُ بِحَمْدِهِ وَالْمَلَائِكَةُ مِنْ خِيفَتِهِ
Addu’ar tsawa
Tsarki ya tabbata ga Allah wanda tsawa ke tasbihi da yabonsa, kuma mala’iku ma suna yi saboda tsoronsa.
دُعَاءُ زِيَارَةِ الْقُبُورِ
السَّلَامُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ، وَإِنَّا إِنْ شَاءَ اللَّهُ بِكُمْ لَاحِقُونَ وَيَرْحَمُ اللَّهُ الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنَّا وَالْمُسْتَأْخِرِينَ، أَسْأَلُ اللَّهَ لَنَا وَلَكُمُ الْعَافِيَةَ.
Addu’ar ziyarar maƙabarta
Aminci ya tabbata a gare ku, mazauna gidaje daga muminai da musulmai. Lalle mu, idan Allah ya so, za mu haɗu da ku. Allah ya jiƙan waɗanda suka riga mu da waɗanda za su zo daga baya. Ina roƙon Allah lafiya da tsari gare mu da gare ku.
دُعَاءُ نُزُولِ الْمَطَرِ
اللَّهُمَّ صَيِّبًا نَافِعًا
Addu’ar saukar ruwan sama
Ya Allah, ka saukar da ruwan sama mai amfani.
دُعَاءُ رُكُوبِ الدَّابَّةِ أَوْ مَا يَقُومُ مَقَامَهَا ( السَّيَّارَةِ أَوِ الْقِطَارِ أَوِ الطَّائِرَةِ أَوِ السَّفِينَةِ)
بِسْمِ اللَّهِ ، الْحَمْدُ لِلَّهِ ، سُبْحَانَ الَّذِي سَخَّرَ لَنَا هَذَا وَمَا كُنَّا لَهُ مُقْرِنِينَ وَإِنَّا إِلَى رَبِّنَا لَمُنْقَلِبُونَ، الْحَمْدُ لِلَّهِ ، الْحَمْدُ لِلَّهِ ، الْحَمْدُ لِلَّهِ ، اللَّهُ أَكْبَرُ ، اللَّهُ أَكْبَرُ ، اللَّهُ أَكْبَرُ ، سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي فَاغْفِرْ لِي ، فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ.
Addu’ar hawan dabba ko abin da ke maye gurbinta—mota, jirgin ƙasa, jirgin sama ko jirgin ruwa
Da sunan Allah. Godiya ta tabbata ga Allah. Tsarki ya tabbata ga wanda ya hore mana wannan, alhali mu ba mu da ikon hore shi. Lalle mu zuwa ga Ubangijinmu za mu koma. Godiya ta tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah. Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma. Tsarki ya tabbata gare Ka, ya Allah, lalle na zalunci kaina, ka gafarta mini; domin babu mai gafarta zunubai sai Kai.
دُعَاءُ السَّفَرِ
اللَّهُمَّ إِنَّا نَسْأَلُكَ فِي سَفَرِنَا هَذَا الْبِرَّ وَالتَّقْوَى، وَمِنَ الْعَمَلِ مَا تَرْضَى ، اللَّهُمَّ هَوِّنْ عَلَيْنَا سَفَرَنَا هَذَا وَاطْوِ عَنَّا بُعْدَهُ، اللَّهُمَّ أَنْتَ الصَّاحِبُ فِي السَّفَرِ، وَالْخَلِيفَةُ فِي الْأَهْلِ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ وَعْثَاءِ السَّفَرِ وَكَآبَةِ الْمَنْظَرِ وَسُوءِ الْمُنْقَلَبِ فِي الْمَالِ وَالْأَهْلِ.
وَإِذَا رَجَعَ قَالَهُنَّ وَزَادَ فِيهِنَّ ـ" آيِبُونَ ،تَائِبُونَ، عَابِدُونَ ، لِرَبِّنَا حَامِدُونَ"
Addu’ar tafiya
Ya Allah, muna roƙonka a cikin wannan tafiya tamu alheri da takawa, da kuma aikin da kake yarda da shi. Ya Allah, ka sauƙaƙa mana wannan tafiya tamu kuma ka rage mana nisanta. Ya Allah, Kai ne Aboki a tafiya kuma Mai kula da iyali a gida. Ya Allah, ina neman tsarinka daga wahalar tafiya, ganin abin baƙin ciki da dawowa a samu mummunan hali a dukiya da iyali.
Idan ya dawo sai ya faɗi waɗannan kalmomi, ya kuma ƙara: Muna dawowa, muna tuba, muna bautawa, kuma muna gode wa Ubangijinmu.
دُعَاءُ الْمُسَافِرِ لِلْمُقِيمِ
أَسْتَوْدِعُكُمُ اللَّهَ الَّذِي لَا تَضِيعُ وَدَائِعُهُ
Addu’ar matafiyi ga wanda ya rage gida
Na miƙa ku ga Allah wanda abin da aka ajiye a wurinsa ba ya ɓacewa.
دُعَاءُ الْمُقِيمِ لِلْمُسَافِرِ
أَسْتَوْدِعُ اللَّهَ دِينَكَ وَأَمَانَتَكَ ، وَخَوَاتِيمَ عَمَلِكَ زَوَّدَكَ اللَّهُ التَّقْوَى، وَغَفَرَ ذَنْبَكَ، وَيَسَّرَ لَكَ الْخَيْرَ حَيْثُ مَا كُنْتَ
Addu’ar wanda ya rage gida ga matafiyi
Na miƙa addininka, amanarka da ƙarshen aikinka ga Allah. Allah ya tanadar maka da takawa, ya gafarta maka zunubinka, kuma ya sauƙaƙa maka alheri a duk inda kake.
دُعَاءُ النُّزُولِ فِي مَكَانٍ
أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ
Addu’ar sauka a wani wuri
Ina neman tsari da cikakkun kalmomin Allah daga sharrin abin da ya halitta.
الدُّعَاءُ بَيْنَ السَّجْدَتَيْنِ
رَبِّ اغْفِرْ لِي رَبِّ اغْفِرْ لِي اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي ، وَارْحَمْنِي وَاهْدِنِي وَاجْبُرْنِي وَعَافِنِي وَارْزُقْنِي وَارْفَعْنِي
Addu’ar tsakanin sujada biyu
Ya Ubangijina, ka gafarta mini; ya Ubangijina, ka gafarta mini. Ya Allah, ka gafarta mini, ka ji ƙaina, ka shiryar da ni, ka gyara min al’amurana, ka ba ni lafiya, ka azurta ni, kuma ka ɗaukaka ni.
دُعَاءُ مَنِ اسْتَصْعَبَ عَلَيْهِ أَمْرٌ
اللَّهُمَّ لَا سَهْلَ إِلَّا مَا جَعَلْتَهُ سَهْلًا وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلًا
Addu’ar idan al’amari ya yi wahala
Ya Allah, babu mai sauƙi sai abin da ka sauƙaƙa, kuma idan ka so kana sa abin da yake da wahala ya zama mai sauƙi.
دُعَاءُ الْخَوْفِ مِنَ الشِّرْكِ
اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أُشْرِكَ بِكَ وَأَنَا أَعْلَمُ ، وَأَسْتَغْفِرُكَ لِمَا لَا أَعْلَمُ
Addu’ar neman tsari daga shirka
Ya Allah, ina neman tsarinka daga in haɗa Ka da wani ina sane, kuma ina neman gafararka ga abin da ban sani ba.
مَا يُقَالُ فِي الْمَجْلِسِ
رَبِّ اغْفِرْ لِي وَتُبْ عَلَيَّ إِنَّكَ أَنْتَ التَّوَّابُ الْغَفُورُ (100 مَرَّةٍ قَبْلَ أَنْ يَقُومَ)
Abin da ake faɗa a majalisa
Ya Ubangijina, ka gafarta mini, kuma ka karɓi tubata. Lalle Kai ne Mai karɓar tuba, Mai yawan gafara. (Sau 100 kafin a tashi)
كَفَّارَةُ الْمَجْلِسِ
سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ ، أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ
Kafarar majalisa
Tsarki ya tabbata gare Ka, ya Allah, kuma yabo ya tabbata gare Ka. Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ina neman gafararka kuma ina tuba gare Ka.
دُعَاءُ مَنْ رَأَى مُبْتَلًى
الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي عَافَانِي مِمَّا ابْتَلَاهُ بِهِ وَفَضَّلَنِي عَلَى كَثِيرٍ مِمَّنْ خَلَقَ تَفْضِيلًا
Addu’ar ganin wanda aka jarabce shi
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya tsare ni daga abin da ya jarabce shi da shi, kuma ya fifita ni a kan yawancin waɗanda ya halitta.
دُعَاءُ الْغَضَبِ
أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ
Addu’ar fushi
Ina neman tsarin Allah daga shaiɗan jefaffe.
الدُّعَاءُ لِلْمُتَزَوِّجِ
بَارَكَ اللَّهُ لَكَ ، وَبَارَكَ عَلَيْكَ ، وَجَمَعَ بَيْنَكُمَا فِي خَيْرٍ
Addu’a ga wanda ya yi aure
Allah ya sanya maka albarka, ya saukar maka da albarka, kuma ya haɗa ku biyu a cikin alheri.
دُعَاءُ الْمُتَزَوِّجِ لِنَفْسِهِ
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ ، وَإِذَا اشْتَرَى بَعِيرًا فَلْيَأْخُذْ بِذُرْوَةِ سَنَامِهِ وَلْيَقُلْ مِثْلَ ذَلِكَ
Addu’ar mai aure ga kansa
Ya Allah, ina roƙonka alherinta da alherin halin da ka halicce ta a kansa. Ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin halin da ka halicce ta a kansa. Idan kuma ya sayi raƙumi, ya riƙe saman tozonsa ya faɗi irin wannan.
الدُّعَاءُ قَبْلَ الْجِمَاعِ
بِسْمِ اللَّهِ ـ اللَّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا
Addu’ar kafin saduwa
Da sunan Allah. Ya Allah, ka nisantar da mu daga shaiɗan, kuma ka nisantar da shaiɗan daga abin da za ka azurta mu da shi.
دُعَاءُ الْعُطَاسِ
إِذَا عَطَسَ أَحَدُكُمْ فَلْيَقُلْ : الْحَمْدُ لِلَّهِ ، وَلْيَقُلْ لَهُ أَخُوهُ ، أَوْ صَاحِبُهُ : يَرْحَمُكَ اللَّهُ فَإِذَا قَالَ لَهُ : يَرْحَمُكَ اللَّهُ ، فَلْيَقُلْ : يَهْدِيكُمُ اللَّهُ وَيُصْلِحُ بَالَكُمْ.
Addu’ar atishawa
Idan ɗayanku ya yi atishawa, ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah. Sai ɗan’uwansa ko abokinsa ya ce masa: Allah ya ji ƙanka. Idan ya ce masa haka, wanda ya yi atishawar ya ce: Allah ya shiryar da ku kuma ya gyara halinku.
الدُّعَاءُ عِنْدَ إِفْطَارِ الصَّائِمِ
ذَهَبَ الظَّمَأُ ، وَابْتَلَّتِ الْعُرُوقُ ، وَثَبَتَ الْأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللَّهُ
Addu’ar mai azumi lokacin buɗa-baki
Ƙishirwa ta tafi, jijiyoyi sun jiƙe kuma an tabbatar da lada, idan Allah ya so.
الدُّعَاءُ إِذَا أَفْطَرَ عِنْدَ أَهْلِ بَيْتٍ
أَفْطَرَ عِنْدَكُمُ الصَّائِمُونَ ، وَأَكَلَ طَعَامَكُمُ الْأَبْرَارُ ، وَصَلَّتْ عَلَيْكُمُ الْمَلَائِكَةُ
Addu’a idan an yi buɗa-baki a gidan wasu
Masu azumi su yi buɗa-baki a gare ku, mutanen kirki su ci abincinku, kuma mala’iku su yi muku addu’a.
دُعَاءُ رُؤْيَةِ الْهِلَالِ
اللَّهُ أَكْبَرُ ، اللَّهُمَّ أَهِلَّهُ عَلَيْنَا بِالْأَمْنِ ، وَالْإِيمَانِ وَالسَّلَامَةِ ، وَالْإِسْلَامِ ، وَالتَّوْفِيقِ لِمَا تُحِبُّ وَتَرْضَى رَبُّنَا وَرَبُّكَ اللَّهُ.
Addu’ar ganin sabon wata
Allah ne mafi girma. Ya Allah, ka sa wannan wata ya bayyana a gare mu da aminci, imani, salama, Musulunci da dacewa da abin da kake so kuma ka yarda da shi. Ubangijinmu da Ubangijinka shi ne Allah.
دُعَاءُ مَنْ أُصِيبَ بِمُصِيبَةٍ
إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ اللَّهُمَّ أْجُرْنِي فِي مُصِيبَتِي وَأَخْلِفْ لِي خَيْرًا مِنْهَا
Addu’ar wanda wata musiba ta same shi
Lalle mu na Allah ne kuma gare Shi za mu koma. Ya Allah, ka ba ni lada a cikin musibata kuma ka maye mini gurbinta da abin da ya fi ta alheri.
الدُّعَاءُ لِلْمَرِيضِ فِي عِيَادَتِهِ
لَا بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللَّهُ مَا مِنْ عَبْدٍ مُسْلِمٍ يَعُودُ مَرِيضًا لَمْ يَحْضُرْ أَجَلُهُ فَيَقُولُ سَبْعَ مَرَّاتٍ : أَسْأَلُ اللَّهَ الْعَظِيمَ رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيَكَ إِلَّا عُوفِيَ.
Addu’a ga mara lafiya yayin ziyartarsa
Babu laifi; tsarkakewa ce, idan Allah ya so. Babu wani bawa musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai zo ba, ya ce sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma, Ubangijin Al’arshi mai girma, ya warkar da kai—face an ba shi lafiya.
دُعَاءُ الْمَرِيضِ الَّذِي يَئِسَ مِنْ حَيَاتِهِ
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي وَأَلْحِقْنِي بِالرَّفِيقِ الْأَعْلَى
Addu’ar mara lafiya wanda ya yanke ƙaunar rayuwa
Ya Allah, ka gafarta mini, ka ji ƙaina, kuma ka haɗa ni da abokan zama maɗaukaka.
مَا يُعَوَّذُ بِهِ الْأَوْلَادُ
أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لَامَّةٍ
Addu’ar neman tsari ga yara
Ina neman tsari dominku biyu da cikakkun kalmomin Allah daga kowane shaiɗan da dabba mai cutarwa, da kuma daga kowane ido mai cutarwa.
دُعَاءُ لِقَاءِ الْعَدُوِّ وَذِي السُّلْطَانِ
حَسْبُنَا اللَّهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ
اللَّهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شُرُورِهِمْ
اللَّهُمَّ أَنْتَ عَضُدِي ، وَأَنْتَ نَصِيرِي ، بِكَ أَجُولُ وَبِكَ أَصُولُ وَبِكَ أُقَاتِلُ
Addu’ar haɗuwa da maƙiyi da mai iko
Allah ya ishe mu, kuma Shi ne mafi alherin wakili.
Ya Allah, muna sanya Ka a gabansu kuma muna neman tsarinka daga sharrinsu.
Ya Allah, Kai ne mai ƙarfafa ni kuma Kai ne mai taimakona; da taimakonka nake zagayawa, da taimakonka nake kai farmaki, da taimakonka kuma nake yaƙi.
دُعَاءُ صَلَاةِ الِاسْتِخَارَةِ
قَالَ جَابِرُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا : كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُعَلِّمُنَا الِاسْتِخَارَةَ فِي الْأُمُورِ كُلِّهَا كَمَا يُعَلِّمُنَا السُّورَةَ مِنَ الْقُرْآنِ ، يَقُولُ : ( إِذَا هَمَّ أَحَدُكُمْ بِالْأَمْرِ فَلْيَرْكَعْ رَكْعَتَيْنِ مِنْ غَيْرِ الْفَرِيضَةِ ثُمَّ لْيَقُلْ : اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ ، وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيمِ فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلَا أَقْدِرُ وَتَعْلَمُ وَلَا أَعْلَمُ وَأَنْتَ عَلَّامُ الْغُيُوبِ ، اللَّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ ـ وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ ـ خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي ـ أَوْ قَالَ عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ ـ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ شَرٌّ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي ـ أَوْ قَالَ عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ ـ فَاصْرِفْهُ عَنِّي وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ).
Addu’ar sallar istikhara
Jabir ɗan Abdullahi, Allah Ya yarda da su, ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana istikhara a cikin dukkan al’amura kamar yadda yake koya mana sura daga Alƙur’ani. Yana cewa: “Idan ɗayanku ya yi nufin wani al’amari, ya yi raka’a biyu ba na farilla ba, sa’an nan ya ce: Ya Allah, ina neman Ka zaɓa mini alheri da iliminka, ina neman iko da ikonka kuma ina roƙonka daga falalarka mai girma. Lalle Kai kana da iko, ni ba ni da iko; Kai kana sani, ni ban sani ba; Kai ne Masanin gaibu. Ya Allah, idan Ka san cewa wannan al’amari—sai ya ambaci buƙatarsa—alheri ne gare ni a addinina, rayuwata da ƙarshen al’amarina, ko ya ce a halinsa na yanzu da na gaba, Ka ƙaddara mini shi, Ka sauƙaƙe mini shi, sannan Ka sanya mini albarka a cikinsa. Idan kuma Ka san cewa wannan al’amari sharri ne gare ni a addinina, rayuwata da ƙarshen al’amarina, ko ya ce a halinsa na yanzu da na gaba, Ka kau da shi daga gare ni, Ka kau da ni daga gare shi, Ka ƙaddara mini alheri duk inda yake sannan Ka sa na yarda da shi.”
دُعَاءُ سُجُودِ التِّلَاوَةِ
سَجَدَ وَجْهِي لِلَّذِي خَلَقَهُ ،وَشَقَّ سَمْعَهُ وَبَصَرَهُ بِحَوْلِهِ وَقُوَّتِهِ ( فَتَبَارَكَ اللَّهُ أَحْسَنُ الْخَالِقِينَ )
Addu’ar sujudar tilawa
Fuskata ta yi sujada ga wanda ya halicce ta kuma ya buɗe mata ji da gani da ikonsa da ƙarfinsa. Allah ya ɗaukaka, mafi kyawun masu halitta.
دُعَاءُ الِاسْتِفْتَاحِ
اللَّهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ الْمَشْرِقِ وَالْغَرْبِ ، اللَّهُمَّ نَقِّنِي مِنْ خَطَايَايَ كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، اللَّهُمَّ اغْسِلْنِي مِنْ خَطَايَايَ بِالثَّلْجِ وَالْمَاءِ وَالْبَرَدِ.
سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ وَتَبَارَكَ اسْمُكَ وَتَعَالَى جَدُّكَ وَلَا إِلَهَ غَيْرُكَ.
اللَّهُ أَكْبَرُ كَبِيرًا ، اللَّهُ أَكْبَرُ كَبِيرًا ، اللَّهُ أَكْبَرُ كَبِيرًا ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ كَثِيرًا ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ كَثِيرًا ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ كَثِيرًا ، وَسُبْحَانَ اللَّهِ بُكْرَةً وَأَصِيلًا(ثَلَاثًا) ـ "أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ مِنْ نَفْخِهِ وَنَفْثِهِ وَهَمْزِهِ ".
Addu’ar buɗe salla
Ya Allah, Ka nisanta tsakanina da zunubaina kamar yadda Ka nisanta tsakanin gabas da yamma. Ya Allah, Ka tsarkake ni daga zunubaina kamar yadda ake tsarkake farin tufa daga datti. Ya Allah, Ka wanke ni daga zunubaina da dusar ƙanƙara da ruwa da ƙanƙara.
Tsarki ya tabbata a gare Ka ya Allah, da yabonka. Sunanka ya albarkata, ɗaukakarka ta buwayi, kuma babu abin bautawa da gaskiya waninka.
Allah ne Mafi girma matuƙa, Allah ne Mafi girma matuƙa, Allah ne Mafi girma matuƙa. Godiya mai yawa ta tabbata ga Allah, godiya mai yawa ta tabbata ga Allah, godiya mai yawa ta tabbata ga Allah. Tsarki ya tabbata ga Allah safe da yamma (sau uku). Ina neman tsarin Allah daga shaiɗan, daga busarsa da tofinsa da hura waswasinsa.
دُعَاءُ دُخُولِ السُّوقِ
لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ يُحْيِي وَيُمِيتُ وَهُوَ حَيٌّ لَا يَمُوتُ بِيَدِهِ الْخَيْرُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ (كَتَبَ اللَّهُ لَهُ أَلْفَ أَلْفِ حَسَنَةٍ وَمَحَا عَنْهُ أَلْفَ أَلْفِ سَيِّئَةٍ وَرَفَعَ لَهُ أَلْفَ أَلْفِ دَرَجَةٍ وَفِي رِوَايَةٍ: وَبَنَى لَهُ بَيْتًا فِي الْجَنَّةِ).
بِسْمِ اللَّهِ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَ هَذِهِ السُّوقِ، وَخَيْرَ مَا فِيهَا، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا فِيهَا، اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أُصِيبَ بِهَا يَمِينًا فَاجِرَةً، أَوْ صَفْقَةً خَاسِرَةً.
Addu’ar shiga kasuwa
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya. Mulki nasa ne, yabo kuma nasa ne. Yana rayawa kuma yana kashewa; Shi Rayayye ne, ba Ya mutuwa. Alheri yana hannunsa, kuma Shi Mai iko ne a kan komai. (Allah zai rubuta masa kyawawan ayyuka miliyan ɗaya, Ya share masa munanan ayyuka miliyan ɗaya, Ya ɗaukaka shi da darajoji miliyan ɗaya. A wata riwaya: Ya gina masa gida a Aljanna.)
Da sunan Allah. Ya Allah, ina roƙonka alherin wannan kasuwa da alherin abin da ke cikinta, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin abin da ke cikinta. Ya Allah, ina neman tsarinka daga yin rantsuwar ƙarya a cikinta ko yin ciniki mai hasara.
عِنْدَ فِعْلِ الذَّنْبِ أَوِ ارْتِكَابِ الْمَعْصِيَةِ
كَمَا أَخْبَرَنَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ((مَا مِنْ عَبْدٍ يُذْنِبُ ذَنْبًا فَيَتَوَضَّأُ فَيُحْسِنُ الطُّهُورَ،ثُمَّ يَقُومُ فَيُصَلِّي رَكْعَتَيْنِ ، ثُمَّ يَسْتَغْفِرُ اللَّهَ لِذَلِكَ الذَّنْبِ إِلَّا غُفِرَ لَهُ )).
Lokacin aikata zunubi ko saɓo
Kamar yadda Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya sanar da mu: “Babu wani bawa da zai aikata zunubi, sannan ya yi alwala ya kyautata tsarki, ya tashi ya yi salla raka’a biyu, sannan ya nemi gafarar Allah saboda wannan zunubin, face an gafarta masa.”
الدُّعَاءُ عِنْدَ سَمَاعِ أَصْوَاتِ الْحَيَوَانَاتِ
الدُّعَاءُ عِنْدَ صِيَاحِ الدِّيكِ : (( اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ )). ((إِذَا سَمِعْتُمْ صِيَاحَ الدِّيكِ[مِنَ اللَّيْلِ]،فَاسْأَلُوا اللَّهَ مِنْ فَضْلِهِ فَإِنَّهَا رَأَتْ مَلَكًا وَإِذَا سَمِعْتُمْ نَهِيقَ الْحِمَارِ،فَتَعَوَّذُوا بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ فَإِنَّهَا رَأَتْ شَيْطَانًا)). مُتَّفَقٌ عَلَيْهِ.
الدُّعَاءُ عِنْدَ صِيَاحِ الدِّيكِ وَنَهِيقِ الْحِمَارِ وَنُبَاحِ الْكِلَابِ: (( أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ )).
((إِذَا سَمِعْتُمْ نُبَاحَ الْكِلَابِ وَنَهِيقَ الْحَمِيرِ بِاللَّيْلِ فَتَعَوَّذُوا بِاللَّهِ فَإِنَّهُنَّ يَرَيْنَ مَا لَا تَرَوْنَ)). صَحِيحٌ(صَحِيحُ سُنَنِ أَبِي دَاوُدَ3/961)
Addu’ar jin muryoyin dabbobi
Addu’ar jin carar zakara: “Ya Allah, ina roƙonka daga falalarka.” “Idan kun ji carar zakara da dare, ku roƙi Allah daga falalarsa, domin ya ga mala’ika. Idan kun ji ihu na jaki, ku nemi tsarin Allah daga shaiɗan, domin ya ga shaiɗan.” Bukhari da Muslim suka ruwaito.
Addu’ar jin carar zakara, ihun jaki da haushin karnuka: “Ina neman tsarin Allah daga shaiɗan jefaffe.”
“Idan kun ji haushin karnuka da ihun jakuna da dare, ku nemi tsarin Allah, domin suna ganin abin da ba ku gani.” Sahihi ne (Sahih Sunan Abi Dawud, 3/961).
سَيِّدُ الِاسْتِغْفَارِ
اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ وَأَبُوءُ بِذَنْبِي ، فَاغْفِرْ لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ.
عَنْ شَدَّادِ بْنِ أَوْسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ ( سَيِّدُ الِاسْتِغْفَارِ أَنْ يَقُولَ الْعَبْدُ اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ وَأَبُوءُ بِذَنْبِي ، فَاغْفِرْ لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ ) مَنْ قَالَهَا فِي النَّهَارِ مُوقِنًا بِهَا فَمَاتَ مِنْ يَوْمِهِ قَبْلَ أَنْ يُمْسِيَ فَهُوَ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ وَمَنْ قَالَهَا مِنَ اللَّيْلِ وَهُوَ مُوقِنٌ بِهَا فَمَاتَ قَبْلَ أَنْ يُصْبِحَ فَهُوَ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ . أَخْرَجَهُ الْبُخَارِيُّ.
Shugaban neman gafara
Ya Allah, Kai ne Ubangijina, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ka halicce ni, ni kuma bawanka ne. Ina kan alƙawarinka da wa’adinka gwargwadon ikona. Ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Na amince maka da ni’imarka a kaina kuma na amince da zunubina; Ka gafarta mini, domin babu mai gafarta zunubai sai Kai.
Daga Shaddad ɗan Aus, Allah Ya yarda da shi, daga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Shugaban neman gafara shi ne bawa ya ce: Ya Allah, Kai ne Ubangijina, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ka halicce ni, ni kuma bawanka ne. Ina kan alƙawarinka da wa’adinka gwargwadon ikona. Ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Na amince maka da ni’imarka a kaina kuma na amince da zunubina; Ka gafarta mini, domin babu mai gafarta zunubai sai Kai. Wanda ya faɗe ta da rana yana mai yaƙini da ita, sai ya mutu a ranar kafin maraice, yana daga mutanen Aljanna. Wanda kuma ya faɗe ta da dare yana mai yaƙini da ita, sai ya mutu kafin asuba, yana daga mutanen Aljanna.” Bukhari ne ya ruwaito.
الدُّعَاءُ إِذَا أَحْسَسْتَ بِوَجَعٍ فِي جَسَدِكَ
ضَعْ يَدَكَ عَلَى الَّذِي تَأَلَّمَ مِنْ جَسَدِكَ وَقُلْ: بِسْمِ اللَّهِ ،ثَلَاثًا ،وَقُلْ سَبْعَ مَرَّاتٍ: أَعُوذُ بِاللَّهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ.
Addu’ar jin ciwo a jiki
Ka ɗora hannunka a wurin da ke maka ciwo a jikinka ka ce sau uku: Da sunan Allah. Sannan ka ce sau bakwai: Ina neman tsarin Allah da ikonsa daga sharrin abin da nake ji da abin da nake tsoro.
مَا يَقُولُ وَيَفْعَلُ مَنْ أَذْنَبَ ذَنْبًا
مَا مِنْ عَبْدٍ يُذْنِبُ ذَنْبًا فَيُحْسِنُ الطُّهُورَ ثُمَّ يَقُومُ فَيُصَلِّي رَكْعَتَيْنِ ، ثُمَّ يَسْتَغْفِرُ اللَّهَ إِلَّا غُفِرَ لَهُ
Abin da mai laifi yake faɗa da aikatawa
Babu wani bawa da zai aikata zunubi sannan ya kyautata tsarki, ya tashi ya yi salla raka’a biyu, sannan ya nemi gafarar Allah, face an gafarta masa.
Lokacin karatuA shirye don karatu
0 / 0

Karatun da ka kammala zai bayyana a nan.

An dakatar da karatu

Bayani da tushe

Raba zikiri

WhatsApp Telegram Facebook X
Rubutun da za a raba

A sake farawa?

Wannan zai share ƙidayar yanzu da inda aka tsaya a wannan rukuni. Tarihin kammala karatu zai kasance a adane.

Daga ɗakin hadisai

Hadisi
Narrated `Urwa: When the wall fell on them (i.e. graves) during the caliphate of Al-Walid bin `Abdul Malik, the people started repairing it, and a foot appeared to them. The people got scared and thought that it was the foot of the Prophet. No one could be found who could tell them about it till I (`Urwa) said to them, "By Allah, this is not the foot of the Prophet (ﷺ) but it is the foot of `Umar."
Sahih al-Bukhari

Reference : Sahih al-Bukhari 1390c In-book reference : Book 23, Hadith 145 USC-MSA web (English) reference : Vol. 2, Book 23, Hadith 474 (deprecated numbering scheme)

Karanta hadisi da tushensa