اللَّهُمَّ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَدۡخِلۡنِي بِرَحۡمَتِكَ فِي عِبَادِكَ ٱلصَّٰلِحِينَ.
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ وَالْمُعَافَاةَ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ.
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْهُدَى ، وَالتُّقَى ، وَالْعَفَافَ وَالْغِنَى.
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ عِلْماً نَافِعًا ، وَرِزْقاً طَيِّباً ، وَعَمَلاً مُتَقَبَّلاً.
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي ، وَاهْدِنِي وَارْزُقْنِي ، وَعَافِنِي ، أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنْ ضِيقِ الْمَقَامِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ.
Ya Allah, ya Ubangijina, Ka ba ni ikon gode maka a kan ni’imarka da Ka yi mini da kuma iyayena, in yi aiki na ƙwarai da Ka yarda da shi, kuma Ka shigar da ni da rahamarka cikin bayinka salihai.
Ya Allah, ina roƙonka yafiya, lafiya da kariya a duniya da lahira.
Ya Allah, ina roƙonka shiriya, taƙawa, kamewa daga haram da wadatuwa.
Ya Allah, ina roƙonka ilimi mai amfani, arziki mai kyau da aikin da aka karɓa.
Ya Allah, Ka gafarta mini, Ka shiryar da ni, Ka azurta ni kuma Ka ba ni lafiya. Ina neman tsarin Allah daga ƙuncin wurin tsayuwa a Ranar Alƙiyama.
"لَّآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنتَ سُبۡحَٰنَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ٨٧". [الْأَنْبِيَاءِ - 87].
“Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ni na kasance daga azzalumai.” [Al-Anbiyaa 21:87]
"رَبَّنَا مَا خَلَقۡتَ هَٰذَا بَٰطِلٗا سُبۡحَٰنَكَ فَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ١٩١ رَبَّنَآ إِنَّكَ مَن تُدۡخِلِ ٱلنَّارَ فَقَدۡ أَخۡزَيۡتَهُۥۖ وَمَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٖ١٩٢ رَّبَّنَآ إِنَّنَا سَمِعۡنَا مُنَادِيٗا يُنَادِي لِلۡإِيمَٰنِ أَنۡ ءَامِنُواْ بِرَبِّكُمۡ فَـَٔامَنَّاۚ رَبَّنَا فَٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرۡ عَنَّا سَيِّـَٔاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ ٱلۡأَبۡرَارِ١٩٣ رَبَّنَا وَءَاتِنَا مَا وَعَدتَّنَا عَلَىٰ رُسُلِكَ وَلَا تُخۡزِنَا يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ إِنَّكَ لَا تُخۡلِفُ ٱلۡمِيعَادَ١٩٤ ". [آلُ عِمْرَانَ - 191-194].
“Ya Ubangijinmu, ba Ka halicci wannan a banza ba. Tsarki ya tabbata a gare Ka, don haka Ka tsare mu daga azabar Wuta. Ya Ubangijinmu, lalle wanda Ka shigar da shi Wuta, hakika Ka wulakanta shi, kuma azzalumai ba su da mataimaka. Ya Ubangijinmu, mun ji wani mai kira yana kira zuwa ga imani: Ku yi imani da Ubangijinku, sai muka yi imani. Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana zunubanmu, Ka kankare mana munanan ayyukanmu, kuma Ka karɓi rayukanmu tare da nagari. Ya Ubangijinmu, Ka ba mu abin da Ka yi mana alkawari ta bakin manzanninKa, kuma kada Ka wulakanta mu a Ranar Alƙiyama. Lalle Kai ba Ka saɓa alkawari.” [Ali Imran 3:191–194]
Azkar na yau da kullum, ba tare da intanet ba. Kyauta.
Android · iPhone · iPad